Isa ga babban shafi
Afghanistan

An kashe wani komandan Taliban da dogaransa a Afganistan

A wani samame da dakarun NATO suka kai a daren jiya Alhamis a Chahar Dara dake yankin arewacin Afganistan, sun samu nasarar kashe kwamandan kungiyar Taliban Mawlawi Bahadur Kamar yadda jimi’in ‘yan sandan yankin Haroon Aryayenezhad ya sanar.A cewar Aryayenezhad, Mulla Bahadur shi ne Gwamnan Taliban da ke kula da yankin arewacin Afganistan kuma daya daga cikin dogarinsa na daga cikin wadanda suka mutu tare da raunana mutane hudu a samamen da aka kai a fadarsu.Kungiyar Taliban dai na yaki ne kan kalubalantar shekaru tara da dakarun NATO 140,000 ke yi wajen hannunta samar da tsaro ga gwamnatin Afganistan a shekarar 2014.Tuni dai daruruwan dakarun NATO suka kaddamar da yaki da yankin Kunduz domin karya matsugunin ‘yan Taliban daga yankin arewacin Afganistan da suka mamaye. 

Dakarun kare zaman lafiya na Afghanistan
Dakarun kare zaman lafiya na Afghanistan ©Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.